22 Mayu 2025 - 21:43
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Kai Hari Kudancin Labanon 

A 'yan mintoci kadan da suka gabata gwamnatin sahyoniyawan ta kai hari kan wani gini a kudancin kasar Labanon.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul Baiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa: Harin da gwamnatin Sahayoniya ta kai bai tsaya kan wani gini kawai ya shafi gurare da dama.

A 'yan mintoci kadan da suka gabata Isra'ila ts kai hari sau biyu ta sama a wajen birnin Tolin da ke kudancin kasar Labanon

Wakilin Al-Mayadeen ya ce: Jiragen yakin gwamnatin yahudawan sahyoniya sun kai wasu jerin hare-hare a yankunan Mahmoudiya, Bargaz, tudun yankin Al-Tuffah da kauyen Buda da ke yankin Beka na kasar Lebanon.

Birnin Tolin na kasar Labanon da aka kai hari a yau yana da tazarar kilomita 35 daga yankunan da aka mamaye kuma yana arewacin kogin Litani.

Your Comment

You are replying to: .
captcha